Bukukuwan cika shekaru 25 da samun 'yancin kan Eritrea

A wannan makon ake cika shekaru 25 tun lokacin da kasar Eritrea ta samu 'yancin kai daga Ethiopia, a wani tashin hankali da aka dauki shekaru 30 ana yi. Kungiyoyin kare hakkin dan-Adam sun soki kasar ta gabashin Afirka game da rashin bin turbar demokradiya da rashin bai wa kafofin yada labarai 'yancinsu da kuma manufofinta na tilastawa mutane shiga aikin soja, wanda ake iya kwashe shekaru masu yawa a ciki. Gwamnatin Eritrea dai ta shirya manyan bukukuwa saboda wannan rana

An dai yi baje kolin tankunan yaki da suka yi tsatsa, da kuma wasu motocin soji da aka kwato daga dakarun Ethiopia a wajen babban birnin kasar.

An dai yi baje kolin tankunan yaki da suka yi tsatsa, da kuma wasu motocin soji da aka kwato daga dakarun Ethiopia a wajen babban birnin kasar.

A wani wajen bikin nuna al'adun gargajiya a Asmara, mutane na sake nuna wasu mahimman abubuwa da suka faru a lokacin yakin da kasar ta yi. Dubun dubatar matan Eritrea sun fafata kafada da kafada da maza a yakin neman 'yancin kai, kuma sune suka kunshi fiye da kashi daya bisa hudu na rundunar sojin da suka yi yakin, har zuwa karshen rikicin. Matan na shiga cikin rundunar sojin, inda ake yanke musu gashinsu kafin su shiga.

An fi sanin yaran da sojojin mata suka haifa a matsayin Red Flowers wato jajayen furanni. Mutane sun ce ana raba yaran da mahaifansu sannan a rene su a wani wajen renon yara saboda iyayensu su cigaba da yaki

An dai kawata gine- gine da dama a fadin kasar, saboda tunawa da ranar samun 'yancin kan

A wani wajen da ake nuna kayayyakin da akai amfani da su a yakin, wannan rigar nonon na daya daga cikin abubuwan da ake nunawa jama'a. An yi ta ne da hannu daga tsummokara. Wani misali ne na irin yadda mayakan Eritrea suke dogaro da kansu da kuma jure rashin kudin da sukai fama da shi a wancan lokacin.

Baya ga rigar nonon, an kuma nuna wani bante. Wani tsohon soja da aka fafata da shi ya ce an yi fama kuma da karancin ruwa na wanke kaya. Ya ce haka kuma akwai karancin sabulu a wancan lokacin, ta yadda ana azabtar da duk wanda ya batar da wani sabulu

Idan kuma aka sallami wadanda suka ji ciwo daga asibiti za ku koma fagen daga, kuma yawanci ba za ka same su da takalmi ba. Likitoci a asibitocin dake karkashin kasa ne suke yin takalma na wucin gadi daga robar da ake karawa marasa lafiya ruwa

Wannan bishiyar na dauke ne da hotunan wadanda suka mutu a yakin su 264, yayinda 'yan tawayen Eritrea suka kusta kai cikin babban birnin kasar Asmara a shekarar 1991

A shekarar 1998, an cigaba da yakin tsakanin Eritrea da kuma Ethiopia. An kashe dubban mutane daga duka bangarorin biyu, a lokacin yakin na shekaru biyu, wanda aka kasa shawo kansa.

Har yanzu Eritrea na alfahari da matsayinta na mai dogaro da kanta, kuma akwai kasuwa ta musamman a Asmara inda ake sake sarrafa karfe zuwa kowanne irin abu da za ka iya tunani. Ana kuma sarrafa tsoffin durom- durom na mai zuwa farantai na cin abinci.

Wannan matashin na aiki ne a wata kofa da aka kera ta wannan hanya. Maza da yawa a kasuwar sun ce har yanzu suna cikin bautawa kasa.

Kodayake bikin nuna al'adun gargajiyar da kuma fareti da ake yi saboda cika wadannan shekaru 25 sun kasance wani taro na farin-ciki ga 'yan Eritrea da dama, amma rayuwar yau da kullum ta kasance mai wahala ga mutane da dama. Yakin da ta yi da Ethiopia ya janyo mata takunkumi da kuma maida ta saniyar ware da kasashen duniya suka yi ya yi wa kasar illa sosai. Amma abubuwa sun soma canzawa

Yanzu haka dai Eritrea na samun karbuwa, inda take samun karin abokan hulda musamman a kasashen larabawa. Kuma ana samun 'yan kasuwar da suke kara zuba jari a kasar musamman a bangaren hakar ma'adinai.

Duk da wannan, majalisar dinkin duniya ta ce 'yan Eritrea dubu biyar ne suke tserewa kasar a kowanne wata, da dama daga cikinsu kuma matasa ne

Tarayyar Turai ta ce ana samun karuwar 'yan Eritrea da suke tafiya Turai fiye da wata kasa a Afirka, da yawa na tserewa ne daga tursasa su da ake yi shiga soja, kodayake hukumomin Eritrea sun musanta hakan.