An kai samame a ofisoshin Google

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin Google da kin biyan harajin $1.8bn.

Jami'an ma'aikatar kudi ta Faransa sun kai samame a ofisoshin kamfanin matambayi-ba-ya-bata na Google da ke Paris game da binciken da suke yi na cuwa-cuwa a biyan haraji.

Rahotanni sun ce ma'aikatan haraji kimanin 100 ne suka kai samame a ofisoshin na Google da ke tsakiyar birnin Paris da safiyar Talata.

Wasu majiyoyin rundunar 'yan sandan birnin sun tabbatar da kai samamen.

Kamfanin na Google ya ce: "Muna yin biyayya ga dokokin Faransa, kuma muna hada kai da hukumomin kasar domin amsa dukkan tambayoyin da za su yi mana."

Ana zargin Google da kin biyan harajin $1.8bn.