Girka: Ana kwashe 'yan hijrar da ke Idomeni

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kimanin masu gudun hijira 8000 ne ake tsare da su a sansanin Idomeni.

Mahukuntan Girka sun fara wani aikin kwashe dubban masu gudun hijira da 'yan ci-ranin da ke sansanin Idomeni, kusa da iyakar kasar da Masadoniya.

Daruruwan 'yan sanda ne suka daka sammako zuwa sansanin don rakiyar 'yan gudun hijirar, wadanda ake kwasa a motocin safa zuwa wasu sansanonin da aka inganta su.

Gwamnatin Girka ta ce za a kwashi kwanaki ana aikin kafin a kammala kwashe 'yan gudun hijirar, kuma 'yan sanda sun ce ba za su yi amfani da karfi wajen kwashe su ba.

Kimanin masu gudun hijira 8000 ne ake tsare da su a sansanin Idomeni, bayan kasar Masadoniya da sauran kasashe sun hana musu wucewa gaba.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Girka Giorgos Kyritsis ya ce za a kai mafi akasarin 'yan gudun hijrar ne zuwa wasu sabbin sansanonin yan gudun hijra da ke kusa da birnin Thessaloniki na kasar Girka.

Mr Kyritsis ya cigaba da cewa ba wai za a kwashe mutanen bane dan a wulkanta su, a'a anyi niyyar hakan ne domin a kyautata rayuwarsu kasancewa a inda suke zama yanzu ba sa jin dadi.

Hukumar tarayyar turai ta shaidawa manema labari cewa ta yi maraba da wannan mataki da Girka ta dauka domin hakan zai kyautata jin dadin rayuwar 'yan gudun hijrar.