Ban nemi mafakar siyasa a Ivory Coast ba – Jonathan

Image caption Ana tuhumar manyan jami'an gwamnatin Jonathan bisa zargin cin hanci.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya musanta rahotannin da ke cewa ya tsere kasar Ivory Coast domin neman mafakar siyasa.

Rahotannin da wata jaridar kasar ta bayar sun ce tsohon shugaban yana cike da bakin cikin, musamman yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari take kama makusantansa bisa zargin almundahana.

A cewar jaridar, rahotannin da tsohon shugaban na Najeriya ya samu sun nua cewa EFCC, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, na shirin kama shi da zarar ya isa Najeriya.

Sai dai tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasar shawara a kan shafukan sada zumunta, Reno Omokri, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ya yi magana da Goodluck Jonathan, inda ya munsata cewa ya nemi mafakar siyasa a kasar ta Ivory Coast.

Ya kara da cewa tsohon shugaban na Najeriya ya je kasar ne domin ya huta kuma da zarar ya kammala abin da yake yi zai koma Najeriya.

Gwamnatin Shugaba Buhari dai ta kama makusanta Mista Jonathan da dama, cikin su har Sambo Dasuki, tsohon mai ba shi shawara kan sha'anin tsaro da Hassan Tukur, tsohon mai yi masa hidima da inda ake zarginsu da warure kudaden kasar.

Haka kuma ana tuhumar tsohuwar ministar man fetur Diezani Allison-Madueke da kuma wasu daga cikin ministocin gwamnatin ta Jonathan bisa zargin cin hanci da rashawa.