Zanga-zanga ta ƙazanta a Kenya

'Yan sanda a kasar Kenya sun ce mutum uku ne suka rasa rayukansu a lokacin da ake zanga-zanga a ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce 'yan sandar Kenyan sun ce an harbe mutum biyu har lahira a garin Siaya da ke yammacin kasar sannan na ukun ya mutu ne a birnin Kisumu bayan ya fadi a lokacin da yake gujewa hayaƙi mai sa ƙwalla.

Sai dai kuma ana ci gaba da samun rahotannin masu cin karo da juna a kan mace-macen.

'Yan sandan sun ƙara da cewa harbe-harben da suka yi a Siaya, na kare kai daga harin 'yan ta'adda ne.