'Yan boko haram na fuskantar shari'a a Nijar

Hakkin mallakar hoto Screen Grab

Nijar ta ce tana tsare da 'yan Boko Haram da dama da yanzu haka take yi wa shara'a.

Shugaban kasar Nijar din, Mohammadou Youssoufou, wanda yake halartar babban taron tallafa wa masu gudun hijira da ake yi a Turkiyya, ya ce za su kiyaye hakkokinsu.

Nijar din dai na daga cikin kasashe masu makwabtaka da Najeriya da ke fama da rikicin na Boko Haram.

Ya kuma yi kira ga dukkan kasashe da su bi sahunsa wajen yin hakan.

A cewarsa wannan ce kadai hanya mafi dacewa ta kare fararen hula.

Mayakan Boko Haram na kai hare-harensu ne a kasashen yankin tafkin Chadi da suka hada da Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

Alhadji Ibrahim Yacouba, ministan harkokin wajen Nijar, ya yi wa BBC karin bayani a kan adadin 'yan Boko Haram din dake fuskantar shara'a a Nijar yanzu haka.