Motoci da jiragen Rasha sun kone a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rasha bata ce komai ba kan lamarin har zuwa yanzu

Wasu hotuna da aka samu ta na'urar dan adam sun nuna cewa jirage hudu masu saukar ungulu, tare da motocin daukar kaya 20, mallakin kasar Rasha, sun kone kurmus a cikin wani sansanin sojoji da ke tsakiyar Syria a makon da ya gabata.

Hukumar tattara bayanan sirrin Amurka Stratfor ce ta fidda hotunan, inda ta ce akwai yiwuwar wani hari ne da kungiyar IS ta kai, ya yi sanadin faruwar lamarin.

Wani masani daga Stratfor din, Sim Tack, ya shaida wa BBC cewa, akwai alamun da ke nuna makarkashiya a lamarin.

Ya ce, "Hotunan sun nuna wurare daban-daban da wuta ta tashi, kuma a gaskia sansanin sojin Rashar ta ji jiki kwarai."

Kungiyar IS din dai bata dauki alhakin harin ba.

Masana dai sun ce ana zaton tartsatsi ne ya dan tashi bayan wani hari da aka kai sansanin, wanda ya yadu zuwa wata tankar man fetur, hakan kuma ya yi sanadin tashin wutar.

Ya zuwa yanzu dai Rasha ba ta ce komai game da lamarin ba.