Ana kokarin fatattakar mayakan IS daga Syria da Iraqi

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar IS na fuskanta manyan hare-hare biyu, a kokarin da ake yi na fatattakar mayakan kungiyar daga Syria da Iraki.

Wani kawancen mayaka, wanda Kurdawa ke jagoranta a arewa-maso-gabashin Syria ya sanar da cewa ana gwabzawa da mayakan IS din a kusa da Rakka.

An dai ce kawancen yana da mayaka 30,000, kuma Amurka da Rasha duka sun yi alkawarin taimakawa.

A Iraki, sojojin gwamnati da mayakan wasu kabilu da suka yi mubaya'a na ci gaba da bude-wuta a kan mayakan IS da ke rike da birnin Fallujah.

Sai dai, wasu majiyoyi na cewa mayakan IS na dakile hare-haren.