Nigeria na son magance tsutsar tumatur

Image caption Tsutsar tumatur ta sa ya yi tsada sosai a Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta dauki matakin yakar cutar tsutsar tumatur, wadda ta kassara noman tumatur a arewacin kasar, tare da haddasa wa manoma asarar makudan kudade.

Ministan noma na Najeriyar, Audu Ogbeh, ta bakin mataimakinsa na musamman kan yada labarai, Dr. Kayode Ayodele, ya ce dole ne gwamnatocin jihohin kasar da al'amarin ya shafa su hada kai da gwamnatin tarayya wajen murkushe cutar tumatur, domin gwamnatin tarayya ita kadai ba za ta iya magance matsalar ba.

Dr Kayode ya lissafa jihohin da cutar tumatir ta gallaba da suka hada Jigawa da Kano da Kaduna da Katsina da kuma Plateau.

Mataimakin ministan na musamman ya kuma yi karin bayani a kan matakan da za a dauka wajen dakile bazuwarta kamar feshin maganin kwari da kuma amfani da sinadaran kashe kwari.

Dr Kayode ya ce ya kamata jihohin da abin ya shafa ma su tashi tsaye, domin wannan matsala bata gwamnatin tarayya ba ce kawai, saboda haka dole ne jihohin da gwamnatin tarayya su hada kai wajen magance wannan matsala.

Manoman rani a Najeriyar dai sun ce suna fuskanci mummunar asarar tumatur sakamakon wata tsutsa da take cinye tumatur din a lokacin da yake gona.