'Ba zan daina sukar gwamnati ba'

Khadija Ismayilova wata 'yar jarida a kasar Azerbaijan
Image caption Khadija Ismayilova wata 'yar jarida a kasar Azerbaijan

Wata fitacciyar 'yar jarida mai binciken kwakwaf a Azerbaijan, Khadija Ismayilova, ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa wajen sukar lamirin gwamnati ba.

Ta yi wannan ikirari ne sa'oi bayan da aka sako ta daga gidan yari a kasar.

Ms Ismayilova ta shaidawa BBC cewa ba za ta rufe idonta kan abinda ke faruwa Azerbaijan din ta yi shiru ba.

An yanke mata hukuncin zaman gidan kaso kan aikata laifuka da suka hada da kaucewa biyan haraji.

Amma kungiyoyin kare hakkin biladama sun ce saboda ta gudanar da bincike kan wasu harkokin kasuwancin iyalan shugaba Ilham Aliyev ne.

Ta dai shafe kimanin shekara guda da rabi a gidan yari.

Sako tan na zuwa bayan da babbar kotun kasar ta yi watsi da hukuncin sakamakon suka daga kasashen waje.