Malaman makaranta na cin hanci a Kenya

Image caption A shekarar 2003 ne Kenya ta kaddamar shirinta na bayar da ilmin firamare kyauta

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kenya ta ce an hada baki da shugabannin wasu makarantun firamare wajen satar kudaden da aka ware wajen shirin bada ilmin firamare kyauta.

Wannan shine rahotan gwamnati na farko da ya bayyana kamarin satar da aka yi a makarantun Kenya.

Ya bayyana yadda aka yi amfani da kudadan da aka ware domin sayen litattafai wajen tafiye-tafiye kasashen waje ba bisa ka'ida ba da kuma amfani da su wajen bai wa iyaye da sauran masu hannu a harkokin tafiyar da makarantu basuka.

An nuna yadda shugabannin makarantu ke samar da kayayyakin aiki ba tare da bayani kan irin kudadan da aka kashe ba.

A cewar rahotan wannan ya shafi karatun dalibai, inda aka tilasta wa kimanin mutane takwas amfani da littafi guda.

'Almubazzaranci'

Ministan ilimi na Kenya Fred Matiangi, ya amsa cewa an tabka almubazzaranci da kudaden harkar ilimi sakamakon rashin sa ido da kyakkyawan tsari na samar da kayayyakin aiki.

Sai dai hukumar tabbatar da da'a ta zargi gwamnatin da gazawa wajan daukar mataki a kan malaman da ake zargi da muna-muna da cin hanci.

Rahotan ya bayar da shawarar samar da ingantattun hanyoyin tabbatar da cewa an kashe kudaden ta hanyar da ya kamata domin rage salwantar kudaden jama'a a makarantun kasar.

A shekarar 2003 ne Kenya ta kaddamar shirinta na bayar da ilmin firamare kyauta, sai dai zargin almundahana da facaka da kudaden ya dabaibaye shi.