Microsoft zai rage guraban ayyuka

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kamfanin Microsoft ya sanar da shirin rage guraban ayyuka har 1,850, a wani bangare na garanbawul a kasuwancinsa na wayoyin komai da ruwan ka.

Kamfanin ya kuma ce zai tanadi ragin dala miliyam dari tara da hamsin ko kuma fan dari shidda da arba'in da shidda, don samun kudaden sallamar ma'aikata.

Wani jami'in kungiyar ma'aikatan ya ce kamfanin ya soke shirinsa na kera karin wayoyin salula, duk da cewa ba a tabbatar da hakan ba.

Matakin na zuwa ne shekaru biyu kacal bayan da kamfanin na Amurka ya biya dala biliyan bakwai kan kasuwancin wayoyin salula samfurin Nokia.

Microsoft din na kuma shirin sayar da kasuwacinsa na sabon samfurin wayoyin Nokia.