An ceto 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto EPA

Dakarun ruwa na Italiya sun ceto ɗaruruwan 'yan gudun hijira bayan jirgin kamun kifi da suke ciki ya soma nutsewa a tekun Bahar Rum.

Dakarun sun hango jirgin ruwan yana tangal-tangal bayan ya taso daga gaɓar tekun Libya.

Jirgin yana cike na maƙil da fasinja da suka riƙa aukawa cikin teku a ƙoƙarin tsira bayan sun hango jirgin dakarun dake ƙoƙarin kawo musu ɗauki.

Mutane fiye da 560 ne suka auka cikin tekun, kuma 7 daga cikinsu sun mutu, amma an ceto sauran baki ɗaya.