Shawo kan mutuwar masu juna biyu a Nijeriya

Hukumomi da kungiyoyin kiwon lafiya a Nijeriya, na kara amfani da ungozomomin gargajiya don shawo kan mutuwar mata masu juna biyu da jarirai.

Shirin muradun cigaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya wato SDGs a Najeriya ne ke baiwa ungozomomin horo kan yadda za su yi aiki a zamanance.

Kana su rika karbar haihuwa tare da kwararrun likitoci, da kuma wayar da kan mata masu juna biyu a unguwannin da suke domin su rika zuwa asibiti a maimakon haihuwa a gida.

Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce mata masu juna biyu 145 ne da kuma jarirai dubu biyu da dari uku, kan rasa rayukansu a Nijeriya a kowace rana saboda rashin kulawar da ta kamata ta lafiya.

UNICEF din ya kuma ce har ma da matsalar karancin kwararrun likitoci da cibiyoyin kiwon lafiya, da ta sanya hukumomin jawo ungozomomi na gargajiya a jika, don su rika bada tasu gudummowa wajen magance matsalar.