Nigeria: Kuɗin shigar gwamnati na raguwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnati ta dogara ne akan kudin shiga daga cinikin mai

Kuɗin shiga da sassan gwamnati a Nigeria suke rabawa kowanne wata ya ragu cikin watan Aprilu da ya gabata.

Ministar kuɗi, Kemi Adeosun ce ta bayyana hakan, inda ta kuma ce hakan na faruwa ne sakamakon faɗuwar da farashin mai ke yi a kasuwar duniya.

Ministar ta ce, daga watan Maris zuwa watan Aprilu kuɗin asusun tarayya ya samu koma bayan fiye da naira biliyan 18.

Gwamnatin Nigeria dai ta dogara ne a kan kuɗin shiga daga cinikin man fetur, wanda yake samar da kashi 70 cikin 100 na kuɗin shigar gwamnati.

Nigeria na fuskantar ƙalubale da suka haɗa da sabon tashin hankali da ake fuskanta a yankin Niger Delta mai arziƙin mai.

Faɗuwar farashin mai ta sa kuɗin shigar jihohi ya ragu sosai, inda wasu jihohin ba sa iya biyan albashin ma'aikatansu.