Xiaomi ya ƙera jirgi maras matuƙi

Hakkin mallakar hoto EPA

Kamfanin ƙera wayar salula na China wato Xiaomi ya bayyana ƙera jirgi maras matuƙi na farko wanda farashinsa yake da sauƙi.

Jirgin mai suna DJI zai iya shawagi a sama tsawon kusan rabin awa, kuma za a riƙa sayar da shi tare da na'urar inganta ɗaukar hoto.

Shiga wannan kasuwa zai baiwa kamfanin Xiaomi damar cimma manufar bunƙasa kasuwancinsa.

Mataimakin shugaban kamfanin na Xiaomi Hugo Barra suna so ne su sayar da na'urar a farashi mai rahusa.

Jirgin maras matuƙi na'ura ce da ake amfani da ita wajen daukar hoto da bidiyo.