Kalubalen tsaro a gwamnatin Buhari

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Sojojin Najeriya na fafatawa da 'yan Boko Haram

Matsalolin tsaro suna daga cikin manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta cikin 'yan shekarun nan.

Rikicin Boko Haram kadai ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu 20, da kuma raba wasu kusan muliyan uku da muhallansu musamman a arewa maso gabashin kasar.

Akwai kuma wasu manyan kalubalen na tsaro baya ga na Boko Haram.

A ci gaba da kawo maku rahotanni da hirarraki kan cikar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shekara guda kan karagar mulkin kasar, wakilinmu Is'haq Khalid, ya duba mana kamun ludayin gwamnatin ta Buhari ta fuskar tsaro.

Ga rahotonsa daga Bauchi:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti