Yaki da cin hanci ta asusun bai daya

A Nigeria daya daga cikin matakan da aka dauka wajen yaƙi da cin hanci da rashawa shi ne bullo da tsarin asusun bai daya na gwamnatin tarayya wato TSA.

Shin ko ya ya tsarin yake? Sannan kuma wacce nasara ko akasin haka aka samu sakamakon amfani da wannan asusun?

A cigaba da rahotannin da muke kawo muku kan cika shekara guda cur da rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Najeriya, Usman Minjibir ya duba mana tsarin na asusun bai daya.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ga kuma rahotonsa: