Duba kan alkawarin aikin yi da Buhari ya yi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Miliyoyin matasa na fama da rashin aikin yi a Nigeria

A Najeriya karancin ayyukan yi na cikin matsalolin da ke addabar jama'a.

Kiyasi ya sha nuna cewa miliyoyin matasa majiya karfi ne ke zaman kashe wando a kasar, a yayin da wasu karin miliyoyin ke kammala manyan makarantu duk shekara ba tare da samun ayyukan yi ba.

Ganin wannan matsala ce ya sanya gwamnatin shugaba Buhari ta dau alkawarin samar da ayyukan yi ga jama'a musamman matasaa lokacin rantsuwar shan mulki.

To ko kusan shekara daya da kasancewar wannan gwamnati a mulki ta cika wannan alkawari?

Daga Kaduna ga rahoton wakilin mu Nurah Mohd Ringim:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti