Tusk na so a taimaki 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Donald Tusk ya ce a daina sukar Turai kan 'yan gudun hijira.

Shugaban majalisar shugabannin ƙasashen Turai, Donald Tusk, ya yi kira ga ƙasashen duniya su tallafa wajen fuskantar matsalar 'yan gudun hijira.

Donald Tusk ya yi wannan kira ne a jawabin da ya gabatar lokacin taron ƙasashe bakwai da ke kan gaba ta fuskar tattalin arziƙi, wato G7 da ake yi a Japan.

Ya kuma ce masu sukar yadda kasashen Turai suka bullowa matsalar 'yan gudun hijira kamata yi su mayar da hankali ga yadda za su taimaka wajen shawo kan matsalar.

Donald Tusk ya kara da cewa, "Muna so ne kasashen duniya su nuna mana goyon baya, kuma su fahimci cewa, matsalar 'yan gudu hijira ta shafi duniya baki daya".