Yajin aikin ma'aikatan nukiliya a Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tuni kasar ta fara fuskantar karancin fetur.

Ma'aikatan tasoshin nukiliya a Faransa na shirin fara yajin aiki a yayin da ake ci gaba da fargaba kan sauye-sauyen da gwamnati ke yi kan 'yan kwadagon kasar.

Kungiyar ma'aikatan nukiliyar, CGT ta ce ma'aikatan tasoshin nukiliya 16 daga cikin 19 sun amince su shiga yajin aikin na kwana daya.

Tuni dai aka fuskanci karancin fetur a kasar sakamakon yajin aikin da aka kwashe kwanaki ana yi, kuma da ma tasoshin na nukiliya sun rage aikin da suke yi kafin yajin aikin da za su shiga ranar Alhamis.

Firai Ministan Faransa Manuel Valls ya nuna alamar yin sassauci kan gyaran da za a yi wa dokokin kwadago na kasar.