A ba habakar tattalin arziki fifiko —G7

Shugabannin ƙasashe bakwai da suka cigaba ta fuskar tattalin arziƙi G7 sun ce, tabbatar da habbakar tattalin arziƙi shi ya kamata a baiwa fifiko.

Cikin wata sanarwar karshen taron na shekara-shekara da aka yi a Japan kasashen na G7 sun kuma yi alƙawarin tabbatar da cewa, an faɗaɗa kasauwanci tsakanin kasashen duniya.

Sanarwar ƙarshen taron ta kuma yi kiran a dauki matsalar 'yan gudun hijira a matsayin wani ƙalubale ga duniya baki daya.

Shugabannin sun yi alwashin hada kai wajen shawo kan barazanar da tattalin arzkin duniya ke fuskanta da suka hada da hare-haren ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

A sanarwar da suka fitar shugabannin sun yi kira da a fadada kasuwancin kasa da kasa , tare da maida hankalin kasashen nasu wajen kaucewa faduwar darajar kudadensu.

Taron ya bayyana matsalar 'yan cirani ko yan gudun hijira a kasashen Turai a matsayin matsalar da ta shafi duniya baki daya da ke bukatar daukar mataki daga kasashen duniyar.