Za a halastawa maza dukan mata a Pakistan

Image caption Tuni mata sun fara mayar da martani kan lamarin

Wani kwamitin bayar da shawara na majalisar dokokin Pakistan na duba yiwuwar bai wa maza damar dukan matansu.

Kwamitin na tsara daruruwan shawarwari kan sha'anin mata a al'umma.

Daya daga cikin shawarwarin na duba yiwuwar bai wa namiji damar dukan matarsa ba da karfi ba, domin nuna rashin amincewa da yanayin shigarta, da hana shi saduwa da ita ba tare da wani hanzari na addini ba da kuma mu'amalarta da mutanen da ba muharramanta ba.

Ana dai nuna matukar fushi kan muhawarar da malamai ke yi kan batun.

Wata mai yin sharhi a jaridu ta ce irin wadannan matakan za su dace ne kawai da karni na bakwai amma ba a wannan zamanin ba.