Yanzu mutum-mutumi za su iya jin zafi

Masu bincike a kasar Jamus na kirkirar wasu jijiyoyin wucin gadi da za su rika koya wa mutum-mutumi yadda za su rika jin zafi ko kuma ciwo.

Kana za su sa mutum-mutumin su rika sansano duk wata matsala da zata iya kama sassan jikinsu cikin sauri, da kuma kare mutane da ke aiki tare da su.

Domin yin gwajin, masanan sun makala wa kafadun mutum-mutumin wata na'urar yatsa mai sansano yanayin zafi ko wata jijjiga.

Kamar dai yadda jijiyoyin sadarwa na jikin dan adam ke aikewa da sakonnin jin zafi zuwa kwakwalwa, wadannan na wucin gadi za su aike da bayanai ga mutum-mutumin, ta yadda zai iya rarrabe zafi mai tsanani da matsakaici.

Wani masani kan mutum-mutumi daga jami'ar Cambridge Prof Fumiya, ya shaidawa BBC cewa koyar da mutum-mutumi daya daga cikin manyan kalubale ne, amma kuma yana da muhimmanci saboda zai sa su kara zama masu hazaka.