Fararen hula na cikin barazanar yunwa a Syria

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun yi kashedin cewa kokarin da suke na kai kayan agaji a yankunan da suka zama fagen daga na gamuwa da cikas.

Majalisar Dinkin Duniya na fatan kai kayan ga mutane miliyan guda dake bukata a cikin watan Mayu.

Amma kuma har yanzu mutane dubu dari da sittin ne kawai aka iya kai wa kayan agajin.

Wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniyar Staffan de Mistura ya ce, fararen hular da dama na fuskantar barazanar fadawa ja'ibar yunwa, muddin dakarun gwamnati da na kungiyoyin 'yan adawa basu bai wa jami'an agajin hanyar shiga ba.

Ya ce matsalar kai kayan agajin jin kan na cikin manyan abubuwan da ke hana ruwa gudu wajen samun zaman tattaunawar sulhu.