Uganda ta kama wasu da laifin kai hari

Image caption An kai harin ne a shekarar 2010

Wani alkali a Uganda ya kama wasu 'yan gwagwarmayar Islama da laifin kai hare-haren bam biyu a wasu mashaya da ake nuna gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Kampala a shekara ta 2010.

Mutane sama da 70 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren.

Alkalin ya samu mutane shida da laifin ya kuma wanke mutane hudu, kuma har yanzu yana yanke hukuncin wasu mutane uku.

Wakilin BBC ya ce alkali Alfonse Owiny-Dollo, ya ce Isa Ahmed Luyima, shine babban wanda ya shirya hare-haran kan klub din wasan zari ruga na rugby da kuma wani gidan abinci a Kamfala.

Shida daga cikin mutanen da ake karar 'yan Kenya ne, biyar 'yan Uganda sai kuma biyu 'yan Tanzaniya.

Sun ce an azabtar da su domin su amsa laifin da ake tuhumarsu, zargin da kotun tsarin mulkin Uganda ta musanta.