Ana tsangwamarmu a India —'Yan Afirka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan Afirka sun bayyana fushinsu sakamakon uzzura musu da ake yi a Indiya

Mai rike da mukamin jakadan Najeriya a India, Sola Enikanolaiye, ya ce bambancin launin fata da ake nuna wa 'yan Afirka da ke zaune a Indiya abin damuwa ne matuka.

Jakadan ya fadi hakan ne a wajen wani taro don bikin Ranar Afirka da Hukumar Kulla Dangatakar Al'adu (ICCR) ta Indiya ta shirya a birnin Delhi ranar Alhamis.

Da farko dai jakadun na kasashen Afirka sun sha alwashin kaurace wa taron, saboda su nuna rashin jin dadinsu game da wani hari da aka kai a kan wani dalibi dan Najeriya a Hyderabad ranar Laraba, da kuma dukan da aka yi wa wani matashi dan kasar Congo har sai da ya mutu a Delhi cikin makon jiya.

Da kyar dai shugaban hukumar ta ICCR, V.K. Singh ya shawo kan jakadun na Afirka suka halarci taron.

Kafin nan dai, jakadun kasashen Afirka a kasar ta Indiya sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa, suna kira da a dauki kwakkwaran mataki a kan "wariyar launin fata da kyamar 'yan Afirka" da ake yi a Indiya.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ta India, PTI, ya ambato Mista Enikanolaiye yana cewa, "abubuwan da suka faru kwanan nan a Bangalore, da Hyderabad, da wanda ya faru makon jiya a Delhi, da ma wasu abubuwa makamantan wadannan a shekaru uku da suka gabata, ciki har da na Goa, suna daga mana hankali sosai.

Ya kara da cewa duk wani batu na 'yan uwantaka da kawance tsakanin India da nahiyar Afirka zai kasance labarin kanzon kurege ne matukar 'yan Afirka ba su da kwanciyar hankali a Indiya.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Indiya ta ce ta bukaci jami'an birnin Hyderabad su ba ta rahoto na gaggawa game da harin da aka kai a kan dalibin dan Najeriya.

Karin bayani