Kotu tayi watsi da ƙarar Simone Gbagbo

Hakkin mallakar hoto AFP

Kotun ƙolin Ivory Coast tayi watsi da ƙarar da mai ɗakin tsohon shugaban kasar, Simone Gabgbo ta ɗaukaka tana ƙalubalantar hukuncin zaman gidan kaso na shekaru ashirin da aka yanke mata.

Bara ne dai aka yankewa Simone Gbagbo wannan hukunci saboda rawar da ta taka a tashin hankalin da ya biyo bayan ƙin amincewa da shan kaye da mijinta yayi a zaɓen shekara ta 2010.

Maigidanta Laurent Gbagbo ma yanzu haka yana fuskantar shari'a a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake birnin Hague.

Ana tuhumarsa ne da aikata laifukan yaƙi dake da alaƙa da rikicin bayan zaben shekara ta 2010.