An aiwatar da wasiyyar Mandela

Mutanen da aka dora wa alhakin aiwatar da wasiyyar tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela sun raba kudi ga ma'aikatansa, da makarantu, da kuma jami'o'in da ya ayyana.

Direban Mandela da ma'aikatan gidansa da ma wadansu hadimansa na daga cikin wadanda za su amfana da kudin, wadanda za su kai dala miliyan daya da dubu dari hudu.

A lokacin da yake raye dai, Nelson Mandela ya sadaukar da wani bangare na dukiyarsa ga fannin ilimi da tarbiyya.

Iyalan Nelson Mandela, wadanda za su samu gadonsu a asirce, sun yaba da yadda ake rabon gadon cikin kwarewa.