Microsoft da Facebook zasu sauƙaƙa sadarwa

Hakkin mallakar hoto EyeWire

Kamfanonin Microsoft da Facebook sun bayyana wani shiri na haɗa Amurka da Turai ta hanyar amfani da manyan wayoyin sadarwa.

Kamfanonin biyu da suka yi fice zasu samar da wani babban kebur da zai taso daga Virginia a Amurka zuwa Bilbao a Spain.

Kamfanin sadarwa na Spain Telefonica ne zai gudanar da aikin.

Idan aka kammala aikin zai saukaka musayar bayanai ta Internet tsakanin Amurka da kasashen Turai.

Wannan aiki dai zai sauƙaƙa musayar bayanai da sadarwa ta Internet.