Za a fara hukunta masu manyan laifuka a Nigeria

Image caption Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban Najeriya.

Gwamnatin Nigeria ta kafa kwamiti na musamman da zai samar da daidaito wajen hukunta waɗanda suka aikata manyan laifuffuka a ƙasar.

Yayin ƙaddamar da kwamitin shugaba Muhammadu Buhari wanda mataimakinsa, Farfesa Yemi Osibanjo ya wakilta ya ce, kwamitin ba zai yi katsalandan a aikin da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa suke yi.

Ministan shari'ah Abubakar Malami ne zai jagoranci kwamitin wanda zai maida hankali wajen tabbatar da cewa, ana yin gaskiya da adalci wajen hukunta waɗanda suka aikata manyan laifuffuka musamman wadanda suka shafi cin hanci da rashawa da ta'addanci.

Farfesa Osinbajo ya ce, alhaki ya rataya akan kwamitin ya tabbatar da cewa, ana hukunta wadanda suka aikata manyan laifuffuka ba tare da nuna son kai ba.

Ya kuma ƙara da cewa, kafa wannan kwamiti ya faru a lokacin da ya dace saboda yadda ake samun ƙaruwar aikata manyan laifuffuka kamar fasa bututun mai a yankin Niger Delta mai arziƙin mai.

A jawabinsa yayin ƙaddamar da kwamitin ministan shari'ah, Abubakar Malami ya ce, kwamitin zai tabbatar ana kaiwa ga hukunta duk wadanda suka aikata mayagun laifuffuka akan lokaci.

Abubakar Malami ya ce, kwamitin zai yi aiki tare da hukumomin dake yaƙi da cin hanci da rashawa da hukumomin tsaro domin tabbatar da ana hukunta wadanda suke aikata manyan laifuffuka cikin gaskiya da adalci kuma ba tare ɓata lokaci ba.

Wannan kwamiti dai zai samar da daidaito da kuma tsari wajen hukunta manyan laifuffuka a Nigeria.