Waiwaiye kan masana'antu a Nigeria

Bangaren masana'antu a Nigeria na cikin ɓangarorin da suka fi fuskantar koma-baya a cikin shekaru da dama.

Hakan dai ya sa a baya an rufe masana'antu da dama a kasar, musamman a arewacin kasar.

Jihar Kano dai na daga cikin manyan cibiyoyin masana'antu na kasar, sai dai a yanzu, sama da rabin masana'antun jihar a rufe suke.

Amma mutane da dama masu aiki a wadannan masana'antu na Jihar Kano na da kyakkyawan fata cewa nan da wani lokaci za a samu kyawawan sauye-sauye da za su farfado da masana'antun da a da suka durkushe.

Ku saurari rahoton wakilinmu, Yusuf Ibrahim Yakasai domin jin karin bayani.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti