MDD: IS na hana farar hula barin Falluja

Hakkin mallakar hoto Ap

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi ammana cewa kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulinci suna hana fararen hula barin Falluja.

Da dama daga cikin fararen hular da suka gudu sun ce an kashe mutane da dama wadanda ke kokarin tserewa, cikinsu har da mata da kananan yara, kuma wadansu ma da rarrafe ta cikin bututan ban ruwa suke guduwa.

Babu isasshen abinci a birnin kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta samu rahotannin mutuwar mutane da dama wadanda suka rasa rayukansu sandiyar matsananciyar yunwa da wasu rahotanni ma na karuwar kisan maza da na yara maza wadanda su ka ki yi wa kungiyar masu tsattsauran ra'ayin aiki.

Kwanaki hudu da suka wuce ne dai gwamnatin Iraki ta sanar da harin da ta kai kan Falluja, kuma tana nuni da cewa sai nan da kwana 20 za ta karbe ikon birnin.

Sai dai Majalisar Dinkin Duniyar ta ce hadarin da ke tattare da hanyar da suke bi su tsere na nufin mutane da dama za su iya rasa rayukansu.