Zika: Ba za a fasa Olympic a Rio ba — WHO

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ma'aikatan lafiya suna feshin maganin rigakafin cutar Zika

Kungiyar lafiya ta duniya WHO ta yi watsi da kiran da kwararru kan lafiya suka yi na a janye wasannin Olympic daga birnin Rio saboda annobar Zika.

A wata budaddiya wasika ga kungiyar ta WHO, kwararrun 150 daga kasashe fiye da gwammai sun ce bai dace a gudanar da wasannin Rio din a watan Agusta ba saboda hadari ga lafiyar al'umma.

Amma a wata sanarwa, WHO din ta yi watsi da kiran da cewa soke ko kuma sauya wurin wasannin ba zai hana yaduwar cutar ta Zika ba.

A cikin wata wasika da suka wallafa, kwararun da suka fito daga gwamman kasashe sun ce a fili take cewa akwai barazana kan lafiyar al'ummar kasashen duniya.

Sun yi kira ga WHO din da ta kafa wani kwamiti na kwararru da zai bai wa kwamitin shirya gasar wasan Olympic din shawarwari.

Kwayar cutar ta Zika dai na saka mata masu juna biyu haihuwar jarirai masu tawaya ko kuma gilo.