Taron Donald Trump ya jawo hargitsi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Magoya bayan Trump sun yi arangama da abokan hamayya, a kan tituna.

Taron da dan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump ya shirya gudanarwa a San Diego na jihar California, ya bar baya da kura.

Mista Trump dai ya je San Diego wanda ke kusa da iyakar kasar Mexico domin yin taro, kafin gudanar da zaben fidda gwani a California, ranar 7 ga Yuni.

Magoya baya sun bar filin taron zuwa tituna, a inda suka yi arangama da bangaren hamayya kuma har ta kai ga an tsamu rashin jituwa da juna.

'Yan sanda sun bayyana duk wani taro da ba a cikin cibiyar gudanar da babban taro ba, da haramtacce.

Sun kuma kama mutane 35 sakamakon jefe-jefe da aka yi da ruwa da duwatsu.