Turai: Tsawa ta hallaka mutum guda da jikkata da dama

Hakkin mallakar hoto AP

Mutum guda ne ya rasa ransa yayinda mutane da dama suka samu munanan raunuka, bayan da tsawa da fada a wasu kasashen Turai.

Tsawar ta hallaka mutane da akasari kananan yara ne a wani wurin shakatawa a birnin Paris, lokacin da suka fake a karkashin wata bishiya yayin wani bikin murnar zagayowar cika shekara.

Mai magana da yawun wani asibiti ya ce yayinda da dama ke murmurewa, yaro guda na cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

A kasar Jamus kuma tsawar ta fada kan wani filin wasan kwallo na yara a lardin Hoppstadten, inda ta jikkata mutane da dama.

A kudancin kasar Poland kuma mutum gude ne ya rasa ransa lokacin da tsawar ta fada masa yayin da yake hawa tsaunuka.