Za mu murƙushe tsagerun Naija Delta — Buhari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Buhari ya sha alwashin murkushe tsagerun Naija Delta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta murƙushe tsagerun yankin Naija Delta, wadanda suke fasa bututan man kasar.

Shugaban, wanda ya bayyana hakan a lokacin jawabin da ya yi wa 'yan kasar ranar Lahadi, ya ce gwamnatinsa ta kaddamar da shirye-shirye domin ci gaban yankin.

A cewarsa, "Haren-haren da masu tayar-da-kayar-baya ke kai wa kan batutan mai da tasoshin samar da hasken wutar lantarki ba za su hana mu tattaunwa da shugabannin yankin Naija Delta ba. Idan wadannan tsageru suna so mu yi arangama da su, to su sani cewa sun yi kuskure, domin kuwa za mu bi su, mu kamo su, sannan mu hukunta su."

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, a cikin shekara daya, gwamnatinsa ta kawo ci gaba a fannoni da dama, yana mai bukatar 'yan Najeriya su ci gaba da hakuri ganin irin mawuyacin halin da ya samu kasar lokacin da ya karbi mulki.