Za a yanke wa Hissene Habre hukunci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana tuhumar Hissene Habre da laifin azabtar da 'yan hamayya.

A ranar Litinin ne ake sa ran wata kotu da ke samun goyon bayan kungiyar tarayyar Afrika a Senegal za ta yanke hukunci a shari'ar da ake yi wa tsohon shugaban Chadi Hissene Habre kan tuhumar da ake masa ta azabtarwa da laifukan yaki.

Hissene Habre shi ne tsohon shugaban kasa na farko a nahiyar Afrika da ake yi wa shari'a a wata kasa.

Masu shigar da kara sun nemi kotun ta yanke masa hukuncin daurin rai-da rai-kan laifukan da 'yan sandansa na sirri suka aikata lokacin da yake mulki daga shekara ta 1982 zuwa shekara ta 1990.

Tsohon shugaban na Chadi ya tsere zuwa Senegal ne bayan da aka hambarar da shi a 1990.

A bara kotun manyan laifuka ta duniya ta umurci Senegal da ta gurfanar da shi ko kuma ta tasa keyarsa domin yi masa shari'a a kasashen waje.