India ta musanta batun wariyar launin fata a kan 'yan Afrika

Hakkin mallakar hoto Getty

'Yan sanda a Indiya sun ce hare-haren da ake kaiwa kan 'yan Afirka da ke birnin Delhi ba su da nasaba da wariyar launin fata.

Wani babban jami'in 'yan sanda Ishwar Singh ya ce abubuwan da suka faru da 'yan Afirkan sun faru ne a wurare daban-daban, kuma a lokuta daban-daban, kuma galibinsu a karamar hayaniya.

Sai dai tsohon shugaban kungiyar dalibai 'yan Afirka da ke karatu a Indiya, Okito Kongo ya shaida wa BBC cewa wariyar launin fata ta zama ruwan-dare a Indiya.

Ya ce ko da 'yan Afirka sun kai kuka ga 'yan sanda, ana nuna musu wariya wajen sauraronsu.

Ya cigaba da cewa idan kana bin titi za ka ji mutane suna aibanta ka da sunan Biri, ko da ka kai kuka wajen 'yan sanda dariyar suke yi, suna kiran ka da Biri

Mutum biyar ne dai 'yan sanda ke tsare da su bisa zarginsu da kai hari kan 'yan Afirka sakamakon kyamar launin fatarsu.

A farkon wannan watan ma sai da aka halaka wani dan Afirka da duka, sakamakon wata gardamar da ta kaure tsakaninsa da mutanen kasar a kan hayar Keke Napep, ko babur mai taya uku.