Syria: Tattaunawar sulhu ta samu cikas

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mohammad Alloush ya yi murabus ne saboda an kasa samo bakin-zaren rikicin Syria.

Babban mai wakiltar 'yan tawaye a kokarin sulhun da ake yi a Syria Mohammad Alloush ya yi murabus sakamakon gazawar da tattaunawar da aka yi ta yi wajen samar da maslaha a rikicin da ya dabaibaye kasar.

Mohammad Alloush ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne ganin cewa tattaunawar da aka yi a Geneva, wadda majalisar dinkin duniya ta shirya, ba ta magance rikicin siyasar Syria ba, ba ta kuma yassare wa al'umara da aka yi wa kawanya wahalhalun da take sha ba.

A watan Afrilun da ya wuce ne kwamitin sulhun ya janye daga tattaunawar, kuma babu wata ranar da aka kebe domin ci gaba da tattaunawar.