Minista ya yi murabus kan cin hanci a Brazil

A Kasar Brazil, Minista na biyu ya yi murabus daga mukaminsa.

Ministan mai suna Fabiano Silveira shi ne mai kula da ma'iakatar da ke yaki da cin hanci da rashawa, kuma ya yi murabus ne bayan an wallafa bayanan da ke cikin wani faifai, inda aka ambato Ministan yana sukar binciken da ake gudanarwa a kan zargin cin hanci a kamfanin man gwamnatin kasar, wato Petrobras.

Mai'aikatan nasa dai sun yi wata zanga-zanga ta hanyar share ma'aikatar tsaf a matsayin alama ta tsabtace ta daga daudar cin hanci, suna bukatar lallai sai ya sauka daga mukaminsa.

A makon jiya ne aka tilasta wa Ministan tsare-tsaren kasar sauka daga mukaminsa, bayan an fitar da irin wannan faifai.

An dai nada Ministoci biyun mukamansu ne bayan dakatar da Dilma Rousseff daga hawa karagar shugabancin kasar.

Ita ma ta dade da zargin cewa an dauki matakin tsige ta daga mukaminta ne da nufin yin cikas ga binciken da ake yi a kan cin hanci da rashawa a kasar.