Ghana: Mutum shida sun mutu a hatsarin kwale-kwale

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu aikin ceto a kogi

Akalla mutum shida ne ake fargabar sun mutu, bayan da kwale-kwalen da dauke da su ya kife a Kogin Volta na kasar Ghana ranar Lahadi.

Mutanen suna daga cikin fiye da mutum 60 da suke tafiya ta kogin daga Nankyeikura zuwa Yeji.

A cewar wasu da suka tsira,kwale-kwalen ya ci karo ne da wani kututture a cikin kogin, abin da ya sa shi yin hatsari.

Kawo yanzu, an ciro gawarwakin mutum shida akasarinsu yara, daga cikin kogin.

Wani dan jarida a Yeji, Daniel Tachie, ya ce wani ayarin masu aikin ceto ya isa inda hatsarin ya auku da yammaci, inda ya ce cikin mutanen da har yanzu ba a gani ba, har da mata masu juna biyu su uku.

Wasu 'yan uwan wadanda lamarin ya ritsa da su suna kukan cewa har yanzu ba su ga 'yan uwan su ba.