Habre zai karashe rayuwarsa a jarun

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon shugaban Chadi Hissene Hebre

Wata kotu a kasar Senegal ta yanke wa tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre hukuncin daurin rai-da-rai bayan ta same shi da laifukan keta hakkin bil adama.

Kotun, wadda kungiyar tarayyar Afirka ke mara wa baya, ta kuma samu Mista Habre da laifukan fyade da bautarwa.

Wannan shi ne karon farko da irin wannan kotun ke zartar da hukunci kan wani tsohon shugaba a nahiyar Afirka.

Tsohon shugaban na Chadi ya musanta cewa ya bayar da umarnin kisan mutum 40,000 lokacin da yake mulki tsakanin 1982 zuwa 1990, yana mai cewa kotun ba ta da hurumin yi masa shari'a.

Ga Raliya Zubairu da karin bayani kan wannan hukunci:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti