An kaddamar da gagarumin farmaki a Falluja

Image caption Mayakan IS ne suka kwace birnin a shekarar 2014.

Sojojin Iraki sun ce sun kaddamar da gagarumin farmaki domin kwato birnin Falluja wanda mayakan kungiyar IS suka mamaye.

Hakan na faruwa ne mako guda bayan gwamnatin kasar ta fara yunkurin kwato birnin, wanda 'yan kungiyar ta IS suka kwace tun daga shekarar 2014.

An kiyasta cewa an rutsa da fafaren hula kusan 50,000 a cikin birnin, ko da ya ke kadan daga cikinsu sun tsere.

Majalisar dinkin duniya ta ce ta samu rahotannin da ke cewa mutane da dama na mutuwa saboda masifar yunwa, yayin da ake kashe wasu saboda sun ki shiga kungiyar ta IS.