Za a habaka harkar noma a Nigeria

Hakkin mallakar hoto

Jihohin arewa maso gabashin Najeriya na shirin kaddamar da wani tsari da zai taimaka wajen habaka harkar noma da mayar da ita abin dogaro ga yankin.

An dai tsakuro shirin ne daga wani kundi da wata tawagar kwararru ta tsara don habaka bangarori daban-daban na tattalin arzikin yankin arewacin Najeriya.

A kwanan baya ne dai dandalin kwararrun masu bincike a bangaren inganta tattalin arziki suka yi wa gwamnoni bitar shirin.

Dokta Usman Bugaje na cikin kwararrun, ya kuma yi wa Muhammad Kabir Muhammad karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti