'Yan Somalia za su sha daurin rai-da-rai

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jirgin Daallo Airlines da a ka tayar da bom a cikinsa

Wata kotun soji a Somalia ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin daurin rai-da-rai, saboda kitsa harin bom a jirgin sama na Daallo Airlines a watan Fabrairu.

Daya daga cikin mutanen, Abdiwali Mahmud Maow, ma'aikaci ne a babban filin jirgin sama, sai kuma Arais Hashi Abdi, wanda ya tsere.

Kotun ta kuma yanke wa wasu mutum takwas, da suka hada da mace guda, hukuncin daurin watanni shida zuwa shekara hudu a gidan kaso.

Fashewar bom din jim kadan da tashin jirgin a Mogadishu, ta kashe maharin sannan ta huda jikin jirgin.

Kungiyar Al-Shabab ta yi ikirarin kai harin, sai dai ta ce bata samu nasarar cimma burinta na kakkabo jirgin kasa ba.