An hana Musulmin Turkiyya ƙayyade iyali

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Erdogan ya yi watsi da shawarar daidaita tsakanin maza da mata.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi kira da musulmin ƙasar da su ƙyamaci ƙwayoyin hana haihuwa, yana mai yin kira a gare su da su ci gaba da hayayyafa.

A wani jawabi da ya yi ta gidan talabijan din kasar, Mista Erdogan ya ce kar wani iyali ya yi tunanin tsayar da haihuwa, maimakon haka ma su rubanya yawan zuri'arsu.

Ya ce "Abin da nake cewa shi ne, za mu hayayyafa, kuma mu rubanya yawan zuri'armu. Suna batun rage yawan al'ummar duniya da tdakatar da haihuwa. Wannan ba na cikakken iyalan musulmi ba ne. Za mu bi dokar Allah ne da tsarin da annabin mu ya shawarce mu."

Kungiyoyin mata dai sun soki furucin da shugaban kasar ya yi a baya, inda ya ce dakatar da haihuwa tamkar cin amanar kasa ce.

Mista Erdogan ya yi watsi da shawarar daidaita tsakanin maza da mata.