Taro a kan fasahar zamani a Nigeria

A ranar Laraba ne ake bude wani taro na kwana uku a kan fasahar zamani a nahiyar Afrika.

Taron, wanda za a yi a Abuja, babban birnin Najeriya zai kuma kunshi baje-kolin kayan fasaha.

Taron na shekara-shekara wani bangare ne na yunkurin mai da nahiyar Afrika ta shiga sahun masu kirkire-kirkiren fasaha maimakon zama mai cin moriyarta kawai.

Haka kuma wata dama ce ta musayar ra'ayi da bayanai kan sabbin kayan fasahar da aka kirkiro ta baya-bayan nan.