Rikicin Biafra ya janyo wa 'yan kasuwa asara

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rikicin ya jawo wa 'yan kasuwa asara sosai

Rahotanni daga kudu maso gabashin Nigeria na cewa al'amurra sun lafa, bayan rikicin da ya barke a sakamakon bikin ranar Biafra da aka gudanar ranar Litinin, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Yanzu haka dai al'umomi mazauna yankin na bayyana irin yadda lamarin ke shafarsu.

Al'ummar arewacin Nigeria da ke gudanar da harkokin kasuwanci a kudu maso gabashin kasar, sun ce sun yi asarar rayukan 'yan uwansu da dama da suka hada da wasu fitattun 'yan kasuwa biyu a yankin.

Kazalika sun ce sun kuma yi asarar kudi fiye da Naira miliyan 10 a rikicin da aka yi ranar Litinin, tsakanin jami'an tsaro da kuma masu fafutukar neman kasar Biafra.

Su ma 'yan kabilar Igbo, 'yan asalin yankin na cewa sun tafka asara mai dinbin yawa a sakamakon rikicin.

Ahmad Abba Abdullahi ya tuntubi wakilinmu na Enugu AbdusSalam Ibrahim Ahmad, domin jin karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti