Mayakan IS na bude wuta a Falluja

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu mayakan IS a Falluja

Mayakan kungiyar IS sun kaddamar da harin mayar da martani inda suka bude wuta da safiyar Talata, a yayin da dakarun gwamnatin Iraki ke cigaba da kokarin kwato garin Falluja.

Wasu manyan hafsoshin sojin Irakin sun ce mayakan kungiyar IS din da yawa sun afkawa dakarun gwamnati kwana daya bayan dakarun sun danna arewacin Nuaimiya.

Majiyar sojin ta ce dakarun sun samu nasarar murkushe mayakan kungiyar, sai dai suma sun ji jiki.

Masu aikin bayar da agaji suna cigaba da nuna damuwa game da makomar fararen hula dubu 50 da suka makale a Falluja.

Rahotanni sun ce wasu mutane a garin na Falluja suna mutuwa saboda rashin abinci, da kuma wasu da mayakan IS ke kashe wa saboda sun ki yarda su shiga cikinsu.